EU ta shimfidawa TikTok wasu sabbin sharudda
June 21, 2022Talla
A wata sanarwar da hukumar da ke kula da kare hakkin masu amfani da kafofin sadarwar zamani ta kungiyar EU ta fidda, ta ce dole ne ire-iren wadannan kafofin sadarwa su tabbatar da cewar duk masu amfani da kafofinsu za su iya gane abubuwan da ke da illa a garesu da ma daukar matakan kare kananan yara.
Bangarorin biyu sun cimma yarjejeniya ne bayan daukar kusan shekara guda suna kai ruwa rana a kan yadda TikTok din zai rika tafiyar da al'amuransa.
A nasa bangaren kamfanin na TikTok zai fidda wata sabuwar hanyar kai kara idan mutum ya ga wani abun da bai dace ba.
Mahukuntan na EU sun sha alwashin saka idanu fiye da na da a kan al'amuran da ke gudana a wannan manhaja da al'umomi ke kuka da ita musamman a nahiyar Afirka.