EU ta yi watsi da buƙatar taimakawa 'yan tawayen Siriya da makamai
February 18, 2013Mafi yawan ƙasashen ƙungiyar Tarayya Turai, sun yi watsi da bukatar ɗage takunkumi shigar da makamai a Siriya, domin taimakawa 'yan tawaye.
A taron da suka shirya yau a birnin Brussels, ƙasashen EU sun ce ɗaukar matakin ɗage takunkumin zai ƙara dagula al'amura a wannan ƙasa da ke fama da yaƙe-yaƙe shekaru biyu kenan da su ka gabata.Ranar ɗaya ga wata mai kamawa, wa'adin takunkumin haramtawa Siriya makamai ke kai ƙarshe saidai EU ta baiyana mahimmancin tsawaita wannan wa'adi.
A wani labarin kuma da ya shafi Siriya,yau ne Komitin da Malisar Dinkin Duniya ta girka domin binciken rikicin Siriya, ya gabatar da rahotonsa a birjin Jeneva na ƙasar Switzerland.
Karla del Ponte, tsohuwar mai shigar da ƙara a kotin ƙasa da ƙasa mai hukunta mayan lefika bugu da ƙari memba a cikin wannan komiti ,ta ce ƙarara sun gano kisan kiyasun da aka aikata a Siriya, kuma lokaci ya yi na gurfanar da masu hannu a cikin wannan ɗanyan aiki gaban kotun ƙasa da ƙasa mai hukunta manyan lefika dake birnin Hague ko kuma La Haye na ƙasar Holland.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal