Dangantaka ta yi tsami tsakanin Turkiyya da Girka
August 26, 2020Ministocin kungiyar tarayyar Turai EU sun kudiri aniyar shiga tsakani, bayan da wata kiki-kaka ta kunno kai tsakanin Turkiyya da kasar Girka kan tekun Bahar Rum. An sanya ranar Alhamis mai zuwa domin tattauna yadda za a kawo karshen ta da jijiyoyin wayar.
Tuni dai shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan a ranar Larabar nan ya murza gashin baki, inda ya ce babu wanda za su daga wa kafa kan batun tekun, saboda mallakinsu ne kuma a shirye suke wajen daukar ko wane irin mataki da ya dace kama tun daga na siyasa har zuwa na soji.
A nata bangaren ministar tsaron Jamus Annegret Kramp-Karrenbauer ta Jamus ta fara duba yadda za a warware bakin zaren lamarin, inda ta ce shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta shirya ganawa da shugaba Erdogan a Juma'a mai zuwa ta wayar tarho.