Kamfanin Facebook zai samar tsarin Internet a Afrika
February 23, 2016Talla
Kamfanin dai ya tabbatar da cewar zai bunkasa harkokin yanar gizo ne kyauata ga wasu yankunan nahiyar Afrika da ba su samu ci-gaba ba ta hanyar tauraron dan Adam.
Shugaban kamfanin Mark Zuckerberg shi ne ya ba da wannan sanarwar a wannan Litinin, a yayin wani taron harkokin sadarwa na duniya a birnin Bercelona na Spain wanda hakan ke zama wani yunkuri na cimma wata yarjejeniya da kamfanin Faransa kan harkokin taurarin dan Adam.
Babban dai kudirin kamfanin na Zuckerberg shi ne ya samar da harkokin yanar gizo kyauta ga wasu yankuna da babu ci-gaba a nahiyar Afrika da wasu yankuna a sassan duniya baki daya da ke zama koma baya wajen harkokin samar da bayanai.