1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafutikar dogaro da kai ta nakasassu a Yuganda

Lateefa Mustafa Ja'afar/GATDecember 2, 2015

Fred Butale dan kasar Yuganda mai Fama da nakasa ya fito da wanni shiri mai taken"the disability Art Project Uganda"domin taimakon nakasassu ta hanyar zane-zane

https://p.dw.com/p/1HFut
Mosambik Thema Behinderung in der Arbeitswelt - Ana Paulo
Hoto: DW/R.d. Silva

A kasar Yuganda wani kiyasi ya nunar da cewa kashi 80 cikin 100 na nakasassu ba su da aikin yi, kasancewar mafi yawansu ba su da isasshen ilimi ko ma ba su da shi kwata-kwata kana iyalansu ma ba sa neman wani abu daga garesu. Baya ga haka rashin isasun kayan aiki a makarantu da za su kula da bukatunsu na taka rawa. Sai dai ga Fred Butale mai kimanin shekaru 30 a duniya ya dauki wariyar da masu nakasa ke fuskanta a matsayin kalubale. Ya yanke shawarar yin wani shiri mai taken "the disability Art Project Uganda" domin taimakon nakasassu ta hanyar amfani da zane-zane.


Yanayin tituna a Kampala babban birnin kasar Yuganda wani babban kalubale ne ga kowa, amma masu nakasa sun fi galabaita. Fred Batale dan shekaru 30 da haihuwa gurgu ne, kuma ya samu nakasa ne sakamakon cutar shan-inna wato Polio da ya kamu da ita tun yana karami kamar yadda ya yi karin haske.

Mosambik Thema Behinderung in der Arbeitswelt - Ana Paulo
Hoto: DW/R.d. Silva

"An haifeni a cikin iyalin da basu da wadata, ina dan shekaru biyar na nakasa, ba ni da kudin sayen keke mai taya-uku, kullum haka ina zuwa makaranta ne ta hanyar yin rarrafe."

Fred ya yi gwagwarmaya ya kuma yi nasarar kammala makaranta da samun gurbin karatu a Jami'ar Makerere. Yanzu yana aiki da kungiyar zane-zane. Bayan aiki, yana kewaya birnin Kampala domin zaburar da masu nakassa karkashin shirinsa na taimako ga nakasassu. Taken shirin kuwa shi ne: "Kada ka karaya duk da nakassa". Shin ko me nene ya ba shi kwarin gwiwa? Batale ya ce:

"Ina ganin saboda ina da sani a kan zane-zane da tsara abubuwa, sai na ke ganin zai iya zame min jagora. A taimaki masu nakasa domin samun abin dogara da kai."

 Duk karshen mako yana amfani da harabar kungiyar da yake aiki domin ganawa da nakasassu, da nufin samar musu hanyoyin dogaro da kai da basu kwarin gwiwa domin zama masu kirkire-kirkire. Suna yin abubuwa kamar kayan ado, da sauransu kana su nemi masu saya. 14 daga cikinsu na da nakasa ta zahiri, hudu daga cikinsu na da matsalar makanta da kurumta, kana ba wai domin su samu kudi ne kawai suke wannan shiri ba. A cewar Manajan shirin Fred Batale, ba abu ne mai sauki ba tafiyar da shirin na nakasassu, ya kara da cewa sakamakon matsalolin kudi galibin kayan da suke amfani da su wajen sarrafa abubuwa, suna samo su ne daga shara da ake zubarwa a kan tituna. Batale ya ce duk da haka yana alfahari da shirin nasa.


"Shirin ya zama abin da nake ji yana tafiya, ina jinsa a jikina. Ina mafarkinsa."

Kawo yanzu suna da hanyar taimako daya, amma mahukuntan birnin Kampala na tunani tallafa musu da kudi. Fatansu shi ne su samu cibiya ta kansu.