1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafutukar yaki da cin hanci a Laberiya

Hirschfeld /Bakarr / NDDecember 30, 2015

Duk da dokar da majalisar dokokin Laberiya ta samar ta hukunta masu aikata laifin cin hanci, ba safai ake hukunta wadanda aka samu da wannan laifi ba.

https://p.dw.com/p/1HVha
DW Sendung Africa on the Move
Hoto: DW

A kasar Laberiya cin hanci da rashawa yayi katutu a al'amuran ayyukan gwamnati duk da cewar majalisar dokokin kasar ta samar da dokar hukunta masu aikata wannan laifi. Sai dai kuma ana zargin cewa ba a hukunta masu aikata wannan laifi, amma wani matashi Jonathan Domah ya kafa wata kungiya mai suna "Central" in da ya daura damarar yakar al'amarin ba da wasa ba.

Karfe takwas na safiya a birnin Monroviya babban birnin Laberiya in da aka gayyaci Jonathan Domah kai tsaye a gidan 'Radio Maria' inda yake wayar da kan jama'a a kan illar cin hanci a cikin harkokin ilimi a Laberiya, yadda malamai a makarantu ke sace kudaden da aka ware domin sayen littattafai.

Gwagwarmayar shimfida adalci a rayuwa

Domah mai shekaru 28 da haihuwa na yin aiki a wata cibiya wadda ke fafutukar ganin an samar da adalci da bin ka'ida wajen tafiyar da al'amura na yau da kullum, kamar yadda ya ce mutane sun dogara da mu ne wajen bayyana musu abubuwan da muka kalato.

"Aikin da muke yana da mahimmanci ga jama'a domin mu kan ba su irin bayanan da muka tattara dangane da irin binciken da muka yi wanda ya shafi cin hanci da rashawa a harkokin ilimi da kuma sauransu."

Amma fa a kowace rana jama'a kan yi maganar cin hanci da rashawa a cikin ma'aikatun gwamnati da kuma tsakanin 'yan siyasa.

Duk da ci gaban da aka samu a Laberiya har yanzu kasar tana a sahun gaba a fannin kididdiga na cin hanci a duniya. Sai dai al'ummar kasar sun fara nuna takaicinsu dangane da albarkatun ma'adanan da Allah Ya basu, amma ba sa gani a kasa.

Belgien Ebola Konferenz in Brüssel
Shugabar Laberiya Ellen Johnson-Sirleaf ta lashi takobin yakii da cin hanci a kasarHoto: T. Charlier/AFP/Getty Images

"Mu al'umma ya kamata mu amfana da arzikin ma'adinai na kasa da Allah Ya bamu, sai dai haka na faskara saboda cin hanci. Cin hanci ya zama karfen kafa a kasarmu, in da ta kai da ya shafi bangaren gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu."

A kowace rana Jonathan Domah ya kan saurari koke-koken al'umma ta cikin shirinsa da ya saba gabatarwa a gidan rediyo. Sai dai a kullum ya kan gaya wa jama'a cewar su kansu za su iya kawo sauyi da kansu.

Hanyoyin sadarwa na zamani na taka muhammiyar rawa

Duk da cewar matashin na amfani da kafar sadarwa ta Facebook da Twitter wajen jawo hankalin mutane a kan ya kamata su san me ake ciki a dangane da yakin da yake yi a kan ta'annati da kudaden jama'a, sai dai kuma ba fa kowa ne ke da zarafin mu'amala da kafar sadarwar ba. Wannan ya sa jama'a suka raja'a wajen sauraron shirinsa na rediyo.

"Mutane ba sa samun damar yin amfani da kafofin sadarwa na zamani, muna da dimbin masu sauraronmu da kuma suke ba da gudunmowa a shirye-shiryenmu."

Tabarbarewar harkar ilimi saboda cin hanci

Sai dai kuma a bangaren harkokin ilimin jami'ar Laberiya akwai maganar karin kudaden makaranta in da dalibai suka koka, don haka Jonathan ya tara shugabannin daliban in da ya bukaci karin haske a kan wasu muhimman batutuwa. Ya kuma yi korafi dangane da halin da jami'ar ta tsinci kanta a ciki na rashin abubuwan inganta ilimin.

Schulen in Liberia öffnen wieder Monrovia 2015
Ana bukatar ingantaccen tsarin ba da ilimi a LaberiyaHoto: DW/J. Kanubah

"Mai aka yi da kudaden da ake karba daga dalibai, wanda za mu ga canji a kasa, duk da cewar babu dakin karatu na zamani da kuma na'urori masu kwakwalwa, dukkannin wadannan babu su a maganar da nake yi yanzu."

Wannan fafutuka da Jonathan Domah ke cigaba da yi a kasar Laberiya ta haifar da sakamako mai kyawun gaske, ganin yadda aka samu canje-canje a fannoni da daman gaske, tare da alkawarin cigaba har sai al'amura sun tafi yadda ya kamata a kasar baki daya.