1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Falasdinawa na cikin mawuyacin hali a Siriya

Muntaqa AhiwaApril 5, 2015

Dubban Falasdinawa ne ke cikin hali na tsaka mai wuya a sansanin hijra na Yarmuk da ke Siriya yankin da a yanzu ke karkashin ikon mayakan IS.

https://p.dw.com/p/1F2pi
Syrien Flüchtlinge Jarmuk
Hoto: picture-alliance/dpa

Kimanin Palasdinawa fararen hula dubu 18 ne ke cikin hali na tsaka mai wuya a sansanin hijra na Yarmuk da ke Siriya, yankin da a yanzu ke karkashin ikon mayakan IS, da kuwa dakarun gwamnati suka yiwa tsinke.

Tuni ma cibiyar dake samar da agaji ga Palasdinawa ta MDD, ta yi kiran a hanzarta kai agaji a yankin, tana mai cewa abin da ke faruwa a Yarmuk, abin kunya ne matuka ga duniya.

Rahotanni sun ce a ranar Laraban da ta gabata ma, 'yan jihadin na IS sun kaddamar da hari kan sansanin na Yarmuk, 'yar tazara da birnin Damascus, suka kuma karbe kusan kashi 90 cikin dari na yankin, duk kuwa da cewar sojojin Palasdinawa sun yi kokarin far musu tun farko.

Yanzu dai wadanda ke wannan wajen, na rayuwa ne irin ta gaba kura, baya sa yaki, kamar yadda Ayman Abu Khashim da ke jagorantar kwamitin kula da Palasdinawa na gwamnatin riko ya sanar.