1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta fara jigilar alhazai

Faruk Muhammad Yabo / LMJAugust 8, 2016

A Najeriya an kaddamar da fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana wadanda zasu samu sauke farali a wannan shekarar a jihar Sokoto.

https://p.dw.com/p/1JdbU
Yadda alhazai ke gudanar da aikin hajji a Saudiya
Yadda alhazai ke gudanar da aikin hajji a SaudiyaHoto: dapd

Sama da maniyyata aikin hajjin bana 50,000 ne za su sauke farali a wannan shekarar daga Najeriya. Bayanai sun nuna cewar akwai filayen jirage 16 da za su yi aikin kwasar alhazan zuwa kasa mai tsarki kuma kamfanonin jiragen sama uku ne aka zaba da suka hadar da Max Air da Fly Nas da Madview Air. Sau tari an sha samun yadda maniyyata aikin hajjin kan nuna halin rashin kamun kai a kasa mai tsarki, amma inji Amirul Hajjin jihar Zamfara a Najeriya kana Sarkin Mafara Alhaji Muhammadu Bello Barmu a bana sun yi kokari na tabbatar da cewar Alhazan jihar basu aikata abin kunya a kasa mai tsarkin ba.

Alhazan Najeriya sun fara tashi zuwa Saudiya
Alhazan Najeriya sun fara tashi zuwa SaudiyaHoto: AMINU ABUBAKAR/AFP/GettyImages

Alhazai sama da 500 a jirgin farko

Jihar Zamfarar dai na da maniyyata aikin hajji 520 da suka tashi a jirgin farko daga cikin sama da 4000 da za su sauke farali a wannan shekarar. Kamfanin jiragen sama na Max Air ne zai fara tashi da alhazan na jihar zamfara, daga cikin alhazai sama da30,000 da kamfanin jiragen saman zai kwasa a wannan shekarar zuwa Saudiyya.