Faransa: Hare-haren IS daga 2015 zuwa yau
Wani mummunan hari da aka kai da wuka a birnin Paris shi ne na baya-bayan nan da kungiyar IS ta dauki alhakin kaiwa a kasar Faransa. Baya ga wannan, a shekaru 3 da suka gabata an kai wasu jerin hare-hare a kasar.
12.05.2018 - Hari da wuka a Paris
Wani mutum dauke da wuka ya raunata mutane a tsakiyar birnin Paris har ya hallaka mutum guda. Masu gabatar da kara a Faransa sun kaddamar da bincike kan harin da ake tunani na ta'addanci ne kasancewar maharin ya ta kabbara gabanin harin kuma kungiyar IS ta dau alhakin kai shi inda ta kira maharin a matsayin guda daga cikin sojojinta.
23.03.2018 - Garkuwa da mutane a birnin Trebes
Wani mahari da ya yi mubayi'a ga IS ya aikata wasu manyan laifuka a birnin Trebes da ke kudancin kasar Faransa.Mutumin ya hallaka wani mazaunin birnin lokacin da ya ke kokarin satar mota sannan ya nude wuta kan 'yan sanda kafin ya shiga wani shagon sayar da kayan abinci inda ya yi garkuwa da mutane. 'Yan sanda sun hallaka mahari, baya ga shi wasu mutum 2 sun rasu sannan wasu 3 suka jikkata.
01.10.2017 - Hari da wuka a tashar jirgin kasa a Marseille
Wani mutum ya dabawa mata biyu wuka a tashar jigin kasa da ke Marseille. Mutumin mai suna Ahmed Hanachi ya rasu bayan da 'yan sanda suka harbe shi. IS ta dauki alhakin kai harin a wani sako da ta fidda. IS ta ce Hanachi daya ne daga cikin sojinta. Wasu ma'aikatan ma'aiaktar harkokin cikin gida su biyu sun aje aiki bayan da aka gano Hanaci na zaune a kasar ba bisa ka'ida ba kuma aka gaza kama shi.
20.04.2017 - Hari kan 'yan sanda a Champs-Elysees
Wani da bindiga ya bude wuta kan 'yan sanda a Champs-Elysees da ke Paris inda ya kashe dan sanda guda da jikkata wasu kafi shi ma daga bisani a kashe shi. An samu wata takarda kusa da gawar maharin da ke nuna goyon baya ga IS kafin daga bisani IS din ta dau alhakin kai harin. Harin ya faru kwanaki kalilan kafin zaben shugaban kasa a Faransa, batun da ya sanya aka tsaurara matakan tsaro a kasar.
03.02.2017 - Hari da adda a Louvre
Sojoji sun yi haribi inda suka raunata wani mutum dauke da adda a wajen gidan adana kayan tarihi na Louvre a birnin Paris bayan da ya kai musu hari. Soja guda ya jikkata. Bincike ya nuna cewar mutumin dan kasar Masar na da alaka da IS bayan da aka gano wasu sakonninsu a shafinsa na Twitter. Mutumin dai ya shiga Faransa ne daga Dubai a matsayin dan yawon bude ido.
26.07.2016 - Kisan wani fada a Normandy
Wasu matasa sun shiga coci a Saint-Etienne-du-Rouvray da ke Normandy inda suka yi wa wani fada mai shekaru 85 da haihuwa yankan rago. An aikata wannan laifin gaban wasu masu ibada su biya. 'Yan sanda sun harbe maharan masu shekaru sha tara yayin da suke kokarin tserewa. IS ta dau alhakin kai harin bayan da ta fidda bidiyon matasa lokacin da suke yi wa kungiyar mubayi'a.
14.07.2016 - Hari da babbar mota a Nice
Wani mutum cikin babbar mota ya danna kai cikin taron jama'a a birnin Nice inda ake shirin kallon wasan kusa da wani tafki. Mutumin ya hallaka mutane 86 da jikkata wajen mutum 400 kafin daga bisani 'yan sanda su harbe shi. IS ta dau alhakin wannan hari inda ta ke cewar maharin ya masa kiranta na kai hari kan kawance kasashen da ke yakar kungiyar a Siriya da Iraki.
13.11.2015: Hare--haren Bataclan da Paris
Shi ne harin ta'addanci mafi muni a Faransa. Mayakan IS dauke da manyan bindigogi da abubuwan fashewa sun kai jerin hare-hare a Paris da kuma gidan Bataclan inda mawaka kan yi wasa. Baya ga wannan sun kuma kai hari filin wasan kwallon kafa fa wasu wuraren shan shayi. Mutane 130 ne suka rasu. Shugaban kasar na wacan loakcin Francois Hollande ya ce hari daidai ya ke da daura damarar yaki da kasar.
21.08.2015: Harin jirgin kasan Thalys da aka dakile
An yi nasarar dakile wani hari da wani ya so kaiwa cikin jirgin kasan Thalys da ya tashi daga Amsterdam zuwa Paris. Wani mutum ne dai ya yi yunkurin bude wuta cikin jirgin amma kunamar bindigar ta makale. Wasu fasinjojin da ke jirgin sun tinkare shi inda suka hana shi aiwatar da harin sai dai mutum hudu sun ji ciwo. Mutumin dama ya yi suna wajen aikata laifuka da suka danganci safarar kwayoyi.
26.06.2015 - Fille kai da kokarin tarwatsa masana'anta a Lyon
Yassin Salhi ya fille kan ubangidansa sannan ya yi rubutun larabci jiki kafin daga bisani ya ajiye kan a gaban wata masana'anta da ke kusa da Lyon. Mutumin ya yi kokarin tarwatsa masana'antar bayan da ya kutsa kai da motarsa kan wasu tukanen gas sai dai bai samu nasara ba. Mutum biyu sun jikkata a haron sannan hukumomi sun alakanta harin da kungiyar IS. Mutumin dai ya kashe kansa a gidan yari.
7 zuwa 9 ga watan Janairun 2015 - Harin Charlie Hebdo
Mutane biyu dauke da manyan bindigogi sun bude wuta a gidan jaridar nan da ke zanen barkwaci ta Charlie Hebdo inda suka kashe mutum12 da raunata da dama. Wani dan bindiga na daban ya kashe dan sanda washegari sannan ya kashe wasu kari hudu a wani shagon sayar da kayan masarufi ranar 9 ga watan Janairu. Daga bisani 'yan sanda sun hallaka maharan wadanda suka nuna goyon bayansu ga kungiyar IS.