150511 Strauss-Kahn Frankreich
May 16, 2011Kame shugaban Asusun ba da lamuni na duniya, Dominique Strauss-Kahn akan zargin yunƙurin yiwa wata mata fyaɗe a birnin New York, ya jefa jam'iyarsa ta 'yan Socialist a Faransa cikin ruɗani tare da buɗe wani makeken giɓi dangane da takarar neman shugabancin ƙasar ta Faransa. Ana ganin Strauss-Kahn mai shekaru 62 a matsayin mutumin da zai ƙalubalanci shugaban Faransa Nikolas Sarkozy a zaɓen ƙasar Faransa dake tafe a baɗi.
Ƙasar Faransa gaba ki ɗaya ta wayi gari ne da wasu hotunan telebijin dake nuna shugaban na Asusun IMF, Dominique Strauss-Kahn a cikin ankwa, 'yan sanda na yi masa rakiya zuwa wurin da za a yi gwajin jikinsa dangane da zargin cin zarafin wata mata a wani otel dake birnin New York. Ya zuwa wannan lokaci ana yi masa kallon na gaban goshi a zaɓen shekara ta 2012 a Faransa.
Ƙarshen rayuwarsa a fagen siyasa?
Yayin da masharhanta gaba ki ɗayansu suka fara yi wa Strauss-Kahn jaje game da abin da suka kira ƙarshen rayuwarsa ta siyasa, su kuwa 'yan siyasa daga dukkan jam'iyun Faransa kira suka yi da ka da a yi riga Malam masallaci wajen ganin laifin shugaban na IMF har sai kotu ta tabbatar da ya aikata wannan laifi na yunƙurin yiwa matar mai shara a otel ɗin fyaɗe. Segolene Royal wadda ke neman tsayawa takarar fid da gwani na jam'iyar 'yan socialist cewa ta yi.
"Kamar ko wane ɗan ƙasa, Dominique Strauss-Kahn yana da 'yancin musanta wannan zargin da ake masa matuƙar babu wata shaida ƙwaƙƙwara. Tunani na na kan iyalinsa da kuma shi kansa da ya shiga cikin wannan mawuyacin hali."
Shi ma tsohon ɗan majalisar dokoki kuma ɗan jam'iyar Socialist Jean-Marie Bockel yana daga cikin 'yan siyasa ƙasar ta Faransa dake saka ayar tambaya ga wannan zargin.
"Wannan ba halinsa ba ne. A matsayin lauya wanda kuma nake har yanzu, ba zan iya yin ƙarin bayani ba."
Labarin kame Strauss-Kahn, dake zama ɗaya daga cikin shugabannin duniya masu angizo, ya jefa Asusun ba da Lamuni na duniya cikin wani hali na tsaka mai wuya musamman gabanin tattaunawar da za a yi game da matsalolin bashi da suka zama ruwan dare a ƙasashen Turai masu amfani da takardun kuɗin Euro.
Fitattun lauyoyi ke kare shugaban na IMF
Strauss-Kahn ya ɗauki manyan lauyoyi da za su kare shi. Ɗaya daga cikin lauyoyin shi ne William Taylor wanda ya faɗawa 'yan jarida a gaban harabar wata kotu dake Manhattan cewa a wannan Litinin za a gurfanar da mutumin da yake karewar gaban kuliya bayan 'yan sanda sun yi gwaje-gwaje a jinkinsa.
"An yi masa wasu gwaje a cikin dare bisa umarnin gwamnati. Amma kasancewa dare yayi a lokacin mun amince a ɗage batun gurfanar da shi har zuwa wannan Litinin, kuma za mu kasance a cikin kotun tare da shi."
Wani kakakin 'yan sanda a New York ya ce tuni sun tuhumi Strauss-kahn da laifin hana walwala ba bisa ƙa'ida ba da yunƙurin aikata laifin fyaɗe akan wata mata 'yar shekaru 32. Matar wadda rahotanni suka ce ta shiga Amirka ne daga ƙasar Gini, ta yi zargin cewa shugaban na IMF ya ci zarafinta lokacin da ya fito ɗakin wanka a otel ɗinsa.
Wannan dai ba shi ne karon farko da aka zarge shi da aikata abin kunya ba, a shekarar 2008 an same shi da yin dadiro da wata 'yar Hungary ma'aikaciyar IMF, amma asusun ya ce bai tilastawa matar ba.
Mawallafa: Johannes Duchrow/Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi