Faransa na son hana dalibai sanya abaya
August 28, 2023Talla
Ministan illimin Faransa Gabriel Attal ne ya sanar da hakan a wata hira a kafar talabijin din kasar. A cewarsa, bai kamata a iya tantance addinin dalibi ba da zarar ka shiga cikin aji.
Tuni dai hukumomi a kasar suka fara nuna maraba da wannan matakin da ministan ya sanar.
An dade ana tafka muhawara kan haramta wa dalibai sanya abaya a kasar. Sai dai kuma wata 'yar majalisa ta bangaren adawa, Clementine Autain ta zargi Faransa da kaurin suna wajen kin jinin musulmi da suka kai kimanin miliyan biyar a kasar.
A shekarar 2004 ne dai aka kafa dokar hana sanya kaya ko wani abu da zai nuna alamar addinin da mutum yake bi.