Faransa ta nesanta kanta da rikicin Libiya
January 5, 2015Talla
Shugaban na Faransa ya ce ya kyautu kasashen su yi abun da ya dace don ganin an samu tattaunawa tsakanin bangarorin, ta yadda za'a mayar da doka da oda a wannan kasa ta Libiya.
Shugaba Hollande na Faransa ya yi wadannan kalamai ne ta gidan radion kasar ta Faransa na France Inter. A baya-bayannan dai, kasashen d ke makwabtaka da kasar ta Libiya da suka hada da Nijar da Chadi, sun yi fatan ganin an dauki matakan soja kan kasar ta Libiya, wadda ake tsoron rikicin n ta zai ci gaba da shafar makwabtanta.