An tilasta Google sake sharuda a Faransa
March 29, 2022Talla
Alkalan wata kotu a binrin Paris sun umarci kamfanin Google ya sake rubuta kwangilolin da yake amfani da su ga masu habaka manhajojin zamani wato "apps developer', bayan da la'akari da cewa kamfanin na kakaba haraji kan kananan kamfanoni.
kamfanin Google ya tilasta wa masu habaka ayyukan fasaha biyan wasu harajin dole har kashi 30 cikin 100 daga kowane tallace-tallace a kan manhajar Play Store.
Alkalan kotun sun baiwa Google watanni uku ya canza sharudan kwangilolin, Google ya ce ya riga ya canza wasu sharuddan kuma tuni ya takaita tasirinsa ga kananan masu fasaha.
Kamfanonin Google Facebook na fuskantar matsin lamba a kasashen duniya musamman Turai saboda zargin cin hanci da rashawa da kuma keta ka'idojin sirrin bayanai.