1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta yi gargadin bazuwar mayakan IS

Fatima Ibrahim Mu'azzam YB
September 11, 2018

Ministan harkokin wajen na Faransa ya ce akwai yiwuwar mayakan sakai daga Faransa da ke cikin al-Ka'ida ko kungiyar IS a birnin Idlib na Siriya su dawo gida.

https://p.dw.com/p/34hah
Syrien Türkisches Militär  (picture-alliance(/dpa/abaca/Anadolu Agency/M. Faysal)
Hoto: picture-alliance(/dpa/abaca/Anadolu Agency/M. Faysal

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya yi gargadi a wannan Talata cewa kokarin ragargaza tungar 'yan tawaye ta birnin Idlib na Siriya zai jawo dubban 'yan ta'adda da ke boye a birnin su watsu zuwa kasashen ketare. Lamarin da ke zama babbar barazana ga kasashen yammacin duniya.

Ministan harkokin wajen na Faransa ya ce akwai yiwuwar mayakan sakai daga Faransa da ke cikin al-Ka'ida ko kungiyar IS a birnin na Idlib su dawo gida. Ministan ya yi wannan jawabi ne ga kafar yada labarai ta BFMTV, ya kuma yi gargadin cewa za a kuma iya samu wasu 'yan ta'addar da za su watsu zuwa kasashe dabam-dabam. Don haka Le Drian ya ce hadakar Siriya da Rasha wajen fatattaka wannan birni na zama barazana ga tsaron kasashensu.