1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa za ta shiga tsakanin Turkiyya da Girka

Binta Aliyu Zurmi
August 13, 2020

Faransa ta sanar da aniyarta ta kara karfin dakarun a yankin tekun Bahar Rum domin rikicin da ke tsakanin Turkiyya da kasar Girka wanda ke da nasaba da makamashi na Gas.

https://p.dw.com/p/3gseU
Frankreich Präsident Emmanuel Macron
Hoto: Getty Images/AFP/L. Marin

Ofishin shugaban na Faransa Emmanuel Macron ya fidda wannan sanarwa bayan da ya yi wata zantawa da takwaransa na Girka Kyriakos Mitsotakis, inda ya baiyyana damuwarsa kan barkewar rikici a yankin. 

To sai dai duk da kokarin da mahukuntan na Paris suka ce suna yi na kara karfin sojinsu a yankin, Shugaba Macron ya ce zaman da dakarunsu za su yi na wucin gadi ne, inda za su sanya idanu don ganin ko za'a mutunta dokar kasa da kasa. 

A jiya Laraba ce, Turkiyya ta aika da injiniyoyinta wajen hakar Iskar Gas din a karo na uku a wannan yanki da ke kudancin kasar ta Girka.