Charles Michel: Bukatar sake kintsa Turai bayan Corona
April 22, 2020Talla
Shugaba Charles Michel na jawabin ne a yayin wata gayyatar da ya yiwa shugabannin kasashe membobi a kungiyar zuwa wani taron koli ta hanyar na'urar sadarwa ta bidiyo a gobe Alhamis. Michel ya ce annobar Corona ta nuna wa kasashen karara irin muhimmancin da ke da akwai na sarrafa abubwan da ake da tsananin bukatarsu a cikin nahiyar, karfafa wa kamfanoni da masana'antun cikin gida domin rage dogaro da wasu da ke waje.
Kalaman shugaban na zuwa ne a yayin da wasu daga cikin kasashen Turan suka fara sassauta dokokin kulle duk da barnar da cutar Corona ta yi mafi muni ga wasu kasashen kungiyar.