1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Salon karbe mulkin 'yan Taliban ya zama abin fargaba a Sahel

Abdoulaye Mamane Amadou
September 10, 2021

Sakatare janar na Malisar Duniya Duniya Antonio Guterres ya nuna fargabar abinda ya faru a Afghanistan ya kasance wani salo ga kungiyoyin masu kaifin kishin addini a yankin Sahel na Kudu da Sahara na Afirka.

https://p.dw.com/p/408u1
UN-Generalsekretär António Guterres
Hoto: Javier Soriano/AFP

A wata tattaunawarsa da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, M. Guterres, ya ce akwai mumunan hadari idan kungiyoyin suka koyi salon matakin karbe iko irin na 'yan Taliban, yana mai cewar dole ne a dauki kwakwaran matakai don kare yankin Sahel da ya kira mai cikakken rauni.

Babban sakataren na Majalisar Dinkin Duniya ya kuma bukaci da a dage tarnakin da rundunar tsaro ta G5 sahel ke fuskanta don tallafa mata wajen tabbataar da tsaron yankin, yana mai cewa matsalar a yanzu ba wai ta tsaya a Mali ko Burkina Faso da Nijar kadai ba ne, a zahiri, ana ganin barazanar har zuwa wasu kasashen makwafta irinsu Ghana da Cote d'ivoire.