Corona: Habasha ta dage zaben 'yan majalisun dokoki
April 1, 2020Talla
Sanarwar hukumar zaben kasar ta ce ta dage zaben saboda wannan annoba ta Corona da ke ci gaba da bazuwa a duniya. Sai dai kuma ba ta sanar da ranar da yanzu za a gudanar da zaben ba.
Ana kallon wannan zabe a matsayin zakaran-gwajin dafi ga mulkin Firaminista Abiy Ahmed don tantance ingancin sauye-sauyen da ya kaddamar a shugabancinsa. Kawo yanzu dai mutane 25 ne Habasha ta tabbatar sun kamu da cutar ta coronavirus a kasar.