Fari da fashi kan teku sun dauki hankullan jaridun Jamus
April 21, 2017Kame jirgin ruwan da aka yi a wannan wata shi ne karo na uku a bana kadai, kusan ko wane wata sai an samu labarin masu fashin tekun sun karkata akalar matafiya kenan. A yanzu dai akwai dakarun kasashen yamma da yawa wadanda ke sintirin hadin gwiwa don yaki da masu fashin teku. Hakan kuwa yasa a shekarun baya lamarin ya yi sauki. Daga cikin rundonin da ke shawagi a tekun Somaliya harda sojojin kungiyar tsaro ta NATO, karkashin Operation Ocean da kuma sojojin kungiyar Tarayyar Turai karklashin Operation Atlanta, haka kuma akwai jiragen ruwa daga kasashen Iran, Saudiyaya, Chaina, da Rasha duk da sunan farautar masu fashi kan teku. Amma bisa ga dukkan alamu masu fashin sun sauya salo.
Matsalar Fari a gabashin Afirka
"Shekara biyu ba'aga ko da digon ruwan sama ba a wasu yankunan gabsashin Afirka. Wannan shi ne labarin jadar die tageszeitung? Jaridar ta ce shekara biyu kenan yankin Somaliland jama'a basu ga damina ba, abinda ya kawo bala'in fari mai muni. Yanzu haka dabbobi da mutane sai mutuwa suke yi. Jaridar ta ce yankin Somaliland wanda ke da kwarya-kwaryan yancin kai, ko da yake ana samun zaman lafiya indan aka kwatanta shi da babbar kasar ta Somaliya, amma wannan fari da ya fadawa kasar da ke tsakiya hamada a gabashin Afirka, za'a iya cewa bala'i ne mai karfi wanda dole sai kasashen duniya sun tashi don shawo kan matsalar, inda yanzu rashin abinci ke haddasa mutuwar jama'a. Musamman tsaffi da yara kanana.
Take hakkokin jama'a a kasar Yuganda
Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung ? Ta duba dokokin tsarin mulki ne kasar Yugunda, inda ta ce koda yake Yugunda kasa ce mai yancin kai, amma tun lokacin da Shugaba Mosevini ya haw kan mulki, babu dokokin kyautata yancin jama'a da aka sauya. Jaridar ta ce abun mamaki shi ne yadda har yanzu a Yuganda ake amfani da dokokin turawan mulkin mallaka daga Ingila, inda ake amfani da su wajen kunttatawa yancin jama'a tamkar a zamanin jahiliya. A yanzu duk wanda ya nuna zai ja da gwamnatin Yuganda, ko da ta kafafen sadarwa na zamani kamar facebook, to ana iya dauko dokokin mulkin mallaka don ladabtar da shi.
Rashin bin ka'idoji daga shugabanni a Afirka
Ita kuwa jaridar Süddeutcher Zeitung tambaya ta yi, wai shin mi yasa kullum ake yi wa kasashen Afirka kallon wadanda ke da matsaloli? Abinda wannan yake nufi shi ne, al'ummomin kasashen Turai ko yaushe sun kasance masu tsaron Afrika. Musamman ga miliyoyin yan Afirka wadanda ake ganin a kwatunan talabijin suna dauke jakunkunansu don zuwa Turai, da zimmar samun rayuwa mai inganci. Jaridar ta ce babban dalilin kwarorowar yan Afirka izuwa Turai ba komai bane illa kawai mafarkin da suke yi cewa Turai wata aljannar duniya ce. Sai a kasashen Afirka makasudin shigarsu yake-yake da talauci, ba komai bane illah rashin shugabannin masu kishin kasa, wadanda ke take tsarin demokaradiyya wadanda ke son kansu da iyalansu kawai.