Fatar Amirka game da zaben 2013 a Kenya
August 4, 2012Sakatariyar harkokin wajen Amirka Hilary Clinton ta yi kira ga kasar Kenya da ta gudanar da zaben da zai samu karbuwa ga kowa da kowa a shekara ta 2013. Ita dai Clinton ta bayyana wannan bukata ne a Nairobi babban birnin kasar, da ke zama zangonta na hudu na rangadin wasu kasashen Afirka da ta ke yi. A cewar sakatariyar ta Amirka, kasarta za ta taimaka wa Kenya shirya zabe mai cike da adalci, domin kauce ma rikicin bayan zabe shugaban kasa, da ya yi awan gaba da rayukan mutane sama da dubu, shekaru fiye da hudun da suka gabata.
Clinton ta gana da shugaban kasa Mwai Kibaki a fadarsa kafin ta yi keke da keke da firaministan Kenya wato Raila Odinga. Kasashe hudu Clinton ta ziyarta i zuwa yanzu ciki kuwa har da Senegal da Uganya da kuma Sudan ta Kudu. Gobe lahadi ne za ta yi tattaki i zuwa Malawi. Kwanaki 12 sakatariyar harkokin wajen za ta shafe a wasu kasashe na Afirka da nufin neman aiwatar da manufofin raya kasashe masu tasowa da gwamnatin Barack Obama ta sa a gaba.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman shehu Usman