Lafiya
Coronavirus ta hana firamnistan Italiya zuwa Afirka
April 18, 2022Talla
Firaminista Mario Draghi na kasar Italiya ya soke ziyarar aiki da aka tsara a kasashen Angola da Congo-Brazzaville, bayan gwaji ya nuna ya kamu da cutar coronavirus.
A wannan Litinin ofishin firamnistan ya bayyana haka, inda sanarwar ta ce Draghi dan shekaru 74 da haihuwa ya nuna alamun kamuwa cutar ta coronavirus gabanin tafiya birnin Luanda na Angola ranar Laraba mai zuwa da kuma birnin Brazzavill na Congo ranar Alhamis, domin tattauna samun makamashin daga kasashen domin maye gurbin wanda kasar Rasha ke mayarwa.
Yanzu dai Luigi Di Maio ministan harkokin wajen kasar ta Italiya da ministan kula da muhalli Roberto Cingolani za su yi tafiyar a madadin firaministan.