1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Firamnistan Japan ya kawar da yuwuwar sake takara

Suleiman Babayo
September 3, 2021

Firaminista Yoshihide Suga na Japan ya ce ba zai sake takara kan neman shugabancin jam'iyyar LDP mai mulki ba, wanda haka yake nuna ba zai sake neman kujerar jagorancin kasar ba.

https://p.dw.com/p/3zs8E
Japan Yoshihide  Suga Präsidentschaftswahl Wahl
Hoto: Taketo Oishi/AP Photo/picture alliance

Firaminista Yoshihide Suga na Japan ya ce yana shirin ajiye aiki. Yayin taron jam'iyyar Liberal Democratic Party, ta LDP da ya wakana a birnin Tokyo, Suga mai shekaru 72 da haihuwa ya ce ba zai nemai shugabancin jam'iyyar ba a karshen wannan wata na Satumba, inda ya rike mukamun na tsawon shekara guda kacal.

Ba zato ba tsammani Firamnista Yoshihide Suga wanda ake gani ba makawa zai sake samun shugabncin jam'iyyar domin ci gaba da jagorancin gwamnatin kasar ta Japan, ya ce ya hakura. Sai dai gwamnatin da yake jagoranci tana shan suka kan yadda ta tunkari annobar cutar coronavirus da ta duniya ta fuskanta.