Fitattun 'yan wasa a gasar Champions League
Fitattun 'yan wasa irin su Cristiano Ronaldo da Lionel Messi da Raúl ne suke kan ganiyarsu a wasan kwallon kafa. Amma wadanne karin ’yan wasa ne ke cikin rukunin manyan goma da suka fi fice a gasar zakarun Turai?
Paolo Maldini - Wasanni 135
Dan wasan baya, Paolo Maldini ya kasance dan wasa mai aminci ga AC Milan, a duk tsawon rayuwarsa ta kwararren dan kwallo. Maldini ya lashe kofin azurfa da ake sha'awarsa sau biyar tare da Milan. A karo biyun farko a shekarar 1989 da 1990 ana kiran gasar da ta cin kofin Turai, yayin da a 1994 da 2003 da 2007 aka kira ta da gasar zakarun Turai.
Sergio Ramos - Wasanni 137*
Sergio Ramos ya lashe kofunan Turai kasa da Maldini. Dan dan kasar Spaniyan ya kammala buga wasanninsa a muhimmiyar gasar tsakanin 2005 zuwa 2021 a Real Madrid. Ya lashe "uwar kofuna" a shekarar 2014 da 2016 da 2017 da 2018. Ramos yana taka leda a Paris St. Germain tun bazarar 2021. (Har zuwa ranar tara ga Maris na 2023)
Thomas Müller - Wasanni 140*
Dan wasan gaba na FC Bayern ya buga wasansa na farko a gasar zakarun Turai a watan Maris na 2009, lokacin yana da shekaru 19. Müller yana cikin sahun 10 na farko ba wai kawai dangane da adadin ayyukan da aka kammala ba, har ma da masu zura kwallo a raga,. Ya lashe kofin Premier sau biyu tare da Bayern. A 2013 a wasan karshe da Dortmund da a 2020 da PSG. (Har zuwa ranar tara ga Maris na 2023)
Raúl - Wasanni 142
Daga 1994 zuwa 2010, Raúl ya taka leda a kungiyar matasa ta Real Madrid a gasar zakarun Turai. Ya lashe gasar ta zakarun Turai sau uku, (1998 da 2000 da 2002). Amma bayan dogon lokaci tare da Madrid, Raúl ya koma Schalke 04 a Bundesliga domin ci gaba da taka leda. Ya kuma yi wasa na dan lokuta a matakin zakarun Turai.
5. Ryan Giggs - Wasanni 145
Da kyar aka samu wanda ya yi wasa a bangaren hagu kamar dan wasan Wales, a gasar zakarun Turai. Giggs ya zama kwararre a Manchester United ranar cikarsa shekaru 17 a duniya, kuma ya buga wasansa na karshe a 2014 yana da shekaru 40. A karkashin mai horas da 'yan wasa Alex Ferguson Giggs ya lashe kofuna 36 tare da 'yan wasa irin David Beckham ciki har da gasar zakarun Turai sau biyu (1999 da 2008).
Karim Benzema - Wasanni 147*
Dan wasan tsakiyar ya taka leda a Olympique Lyon da Real Madrid a gasar zakarun Turai. Bayan tafiyar Cristiano Ronaldo Bafaranshen mai asali da Aljeriya ya zama babban jigo a Real Madrid. Benzema wanda yake daya daga cikin 'yan wasan da suka fi zura kwallaye a gasar ta Turai, ya lashe gasar da Real Madrid sau biyar (2014 da 2016 da 2017 da 2018 da 2022). (Har zuwa ranar tara ga Maris na 2023)
Xavi - Wasanni 151
Zakaran duniya da Turai, yana hada gwiwa da Andrés Iniesta a FC Barcelona karkashin mai horas da 'yan wasa Pep Guardiola wajen ciyar da kungiyarsa gaba. Xavi ne babban jigo a tsarin wasa na tiki-taka da aka san Barça da shi. A karkashin Guardiola ne Xavi ya lashe gasar zakarun Turai sau uku (2006 da 2009 da 2011). A shekarar 2015, ya kara samun kofin karkashin Luis Enrique.
Lionel Messi - Wasanni 163*
A gaban Xavi da Iniesta fitaccen dan wasan Barcelona Lionel Messi yana da damar karyawa inda ba gaba, a wasanni da yawa. Dan Ajentina wanda ya taka rawar gani a Barça tsawon shekaru 17 tun daga 2004, shi ma ya lashe gasar zakarun Turai sau hudu (2006 da 2009 da 2011 da 2015). Messi yana wasa a kungiyar Paris St. Germain tun shekarar 2021. (Har zuwa ranar tara ga Maris na 2023).
Iker Casillas - Wasanni 177
Iker Casillas mai tsaron gidan da tsayinsa ya kai mita 1.82, an karbe shi a Real Madrid yana da shekaru 16. Amma shekaru biyu bayan haka, Casillas ya maye gurbin zakaran duniya Bodo Illgner na Jamus a matsayin mai tsaron gida. Ya lashe gasar zakarun Turai sau uku tare da Real Madrid a (2000 da 2002 da 2014). A shekara ta 2015 ya bar kulob din, kuma ya buga wasanni 27 na zakarun Turai da FC Porto.
Cristiano Ronaldo - Wasanni 183
Dan kasar Portugal wanda ya fafata a gasar zakarun Turai tare da Manchester United da Real Madrid da Juventus a tsawon rayuwarsa, ba wai gwani na gwanaye ne kadai ba amma ya kasance dan wasan da ya fi zura kwallaye a gasar zakarun Turai. Ronaldo ya lashe gasar zakarun Turai a karon farko a 2008 tare da United. Sannan ya lashe karin kofuna hudu tare da Real (2014 da 2016 da 2017 da 2018).