Francois Bozize zai tsaya takara
August 8, 2015A kasar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, jam'iyyar adawa ta Kwa Na kwa ta kaddamar da tsohon shugaban kasar Francois Bozize a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasa da kasar za ta gudanar a watan Oktoba mai zuwa. Wannan mataki ya biyo bayan wani taron congress da jam'iyyar ta KNK ta shirya a ran Juma'a a birnin Bangui.
Taron jam'iyyar ta KNK ya wakana ne ba tare da Francois Bozizen tsohon shugaban kasar ta Jamhuriya Afirka ta Tsakiyar, wanda sojoji suka kifar da mulkinsa a cikin watan Maris din shekara ta 2013 ya halarta ba, kasancewa yana zaman gudun hijra inda ya ke safa da marwa tsakanin kasashen Kenya da Uganda tun daga wancan lokaci.
Kimanin 'yan takara dari ne ke tsayawa takarara neman mukamin shugaban kasa a zaben na watan Oktoba mai zuwa.