Mai kimanin shekaru 30 a duniya Batale na zaune a kan keken guragunsa kuma da haka ne yake kokarin inganta rayuwarsa. Mutanen da ke fama da nakasa na shan wahalar rayuwa a Yuganda. Galibin su ba su da ilimi saboda babu kayan aiki a makarantu da za su kula da bukatunsu.