Fursunoni 900 sun tsere a Kwango
June 11, 2017Talla
Gwamnan Arewacin Kivu Julien Paluku ya ce maharan da ba'a kai ga tantace inda suka fito ba, sun yi amfani da man'yan makamai a yayin harin inda suka kashe jami'ai tsaron gwamnati takwas da kea gadin yarin. Kawo yanzu dai babu kungiyar da ta dau alhakkin harin.
A ranar Asabar da ta gabata wata kafar sadarwar internet a kasar da ma bayanan daga hukumomin 'yan sanda, sun ruwaito wata kungiyar addini da ke labewa da siyasa, mai suna "Bunda dia Kongo", ta kai wani hari a ofishin mai shigar da karan gwamnati tare da kai wani hari a ofishin 'yan sanda da ke Kinshasha babban birnin kasar. A yanzu dai tuni hukumomin tsaro suka ayyana dokar ta-baci a garin na Beni da aka kai harin.