'Yan sanda na cin zarafin jama'a a Afirka
July 7, 2020A kasashen Afirka dubun dubatar mutane ne suka yi zanga-zangar nuna zumunci ga bakaken fatan Amirka da ke shan azaba hannun 'yan sanda. A lokaci daya masu zanga-zangar sun janyo hankali kan cin zarafi da azaba da suke sha hannun 'yan sanda a kasashen Afirka, da ke da asali tun zamanin mulkin mallaka.
Shan azaba a hannun 'yan sanda ya zama ruwan dare sai dai a Afirka dalilan sabanin a Amirka ba na wariyar launi fata ba ne
A makonni bayan nan a wasu manyan biranen kasashen Afirka kamar Kenya, Afirka ta Kudu da Najeriya an gudanar da jerin zanga-zangar adawa da irin gallazawa da azaba da ake sha hannun 'yan sanda. Hakan ya zo ne bayan mutuwar bakar fatan Amirkan nan George Floyd da wani dan sanda ya shake shi har ya kasa numfasawa. A kasashen Afirka da dama shan azaba a hannun 'yan sanda ya zama ruwan dare. Sai dai a Afirka dalilan sabanin a Amirka ba na wariyar launi fata ba ne, a cewar masana irin su Annette Weber masaniya kan gabashin Afirka a gidauniyar Kimiyya da Siyasa da ke birnin Berlin: "Ba a cin zarafinka saboda launin fatarka, sau da yawa talakawa da wasu kabilun da ake nuna musu bambamci a daidaikun kasashe, da ma masu fafatukar kare tsirarun al'umma abin ya fi shafa, duk da cewa su ma 'yan kasa ne kamar kowa. A Kenya ga misali 'yan asalin Somali da ma mazauna gabar teku suka fi jin radadin wannan aika-aika."
'Yan sandar galibi na cin zarafin wanda suka ga alamar ba zai iya daukar lauya ba da zai kare shi
Masaniyar ta kara da cewa a yaki da Corona 'yan sanda sun fi gallazawa talakawa wadanda ba sa iya biyayya sau da kafa da tsauraran matakan kulle da aka dauka. Shi ma Gareth Newham na cibiyar nazarin lamuran tsaro a Afirka da ke birnin Pretoriya na ATK ya tabbatar da haka : "Mafi rinjayen 'yan sanda bakar fata ne, sannan mafi yawan wadanda ke dandana akuba hannun 'yan sandar bakar fata ne musamman matasa. Saboda haka ba za a kira shi da wariyar launin fata a Afrika ta Kudu ba. Lamari ne na matsayinka cikin al'umma. 'Yan sanda sun fi aikata ta'asa a kan talakawa. Idan kana cikin sabuwar mota sanye da kaya kyawawa ka kuma nuna alama za ka iya daukar lauya da zai kare ka, ba za su fuskance ka ba."
Akwai rashin yarda tsakanin 'yan sanda da jama'a, tushen wannan matsalar na da alaka da tarihin mulkin mallaka
A da yawa daga cikin kasashen Afirka dai akwai rashin yarda tsakanin 'yan sanda da jama'a, tushen wannan matsalar na da alaka da tarihin mulkin mallaka, inda aka yi amfani da 'yan sanda wajen aiwatar da dokokin 'yan mulkin mallaka, a cewar masanan.
Ra'ayin masanan ya zo daya cewa ana bukatar nagartaccen tsarin aikin 'yan sanda da ba su kayan aiki na zamani da ba su horo na hakika hade da albashi mai tsoka, matukar ana son a ga sauyi mai ma'ana a aikin jami'an tsaron a Afirka.