1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gambiya: Barrow ya kama hanyar lashe zabe

Zainab Mohammed Abubakar
December 2, 2016

Shugaba Yahya Jammeh da ya dauki tsawon shekaru 22 ya na shugabancin Gambiya, ya amince da shan kaye a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Alhamis daya ga watan Disambar da muke ciki.

https://p.dw.com/p/2TdSg
Gambia Präsidentschaftswahl Adama Barrow
Hoto: Getty Images/AFP/STR

Shugaban hukumar zaben kasar mai zaman kanta wanda ya sanar da haka a wannan Juma'ar, ya ce dan takarar adawa Adama Barrow shi ne ke kan gaba da mafi yawan kuri'u. Gabanin gabatar wa da manema labarai da sakamakon zaben a babban birnin kasar Banjul Alieu, Momar ya ce, Yahya Jammeh ya yi rawar gani na bayyana cewa ya amince da kayen da ya sha kai tsaye bayan kasancewarsa kan kujerar mulki na tsawon shekaru 22. Gidan talabijin na Gambiya ya sanar da cewar, Jammeh mai shekaru 51 da haihuwa, wanda ya kama madafan iko biyo bayan juyin mulki a shekara ta 1994, zai gabatar da jawabin taya murna ga sabon zababben shugaban kasar nan gaba. Adama Barrow ya yi takara a karkashin inuwar jam'iyyun siyasar Gambiya guda takwas bayan sun hade, kuma wannan ita ce takararsa ta farko.