Gambiya: Martani kan matakin Shugaba Jammeh
December 12, 2016Shugaban kasar Gambiya mai barin gado Yahya Jammeh ya sanar da shirin kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar da ya bayyana dan takarar jam'iyyar adawa Adama Barow a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar daya ga watan Disamba. Sai dai jama'a da dama na ganin wannan mataki na Shugaba Jammeh zai jefa yankin cikin rudani da rashin kwanciyar hankali. Da farko dai Shugaba Jammeh ya amince da shan kaye amma daga baya ya sauya matsayinsa.
Shugaba Jammeh ya ce tunda farko ya amince da sakamakon zaben ne saboda a zatonsa hukumar zaben kasar tana aiki ne bisa gaskiya da adalci, amma saboda akasin haka ya sauya matsayi tare da kin amincewa da sakamakon zaben. Kuma tuni Jam'iyyarsa ta APRC mai mulki ta ce tana shirye-shiryen shigar da kara gaban kotu don kalubalantar sakamakon zaben.
Wannan mataki da Yahya Jammeh ya dauka ya sanya jama'a da dama da shugabanin jam'iyyun adawar kasar mayar da martani tare da kira a gareshi kan ya mutunta muradi da zabin 'yan kasar, ta hanyar mika mulki cikin kwanciyar hankali.
Bagan N'Djai dan kasar Gambiya ne da ke zaune a birnin Banjul, ya ce fatansu shi ne su kasance tamkar sauran kasashen duniya wajen samun zaman lafiya, matakin da shugaban kasar tasu ya dauka ba zai kai kasar ga nasara ba.
"Yahya Jammeh shugabanmu ne ya yi mulkinmu shukaru 22. Jama'a sun nemi canji kuma sun samu. Mun gode masa da kokarin da ya yi. Ya yi abubuwa masu kyau da kuma abubuwan da ba su kamata ba, lokaci ya yi da zai sauka ya bada guri, saboda a zauna lafiya. Muna godiya da taya shi murna da kuma rokonsa da ya koma gida ya zauna".
Shugaban jam'iyyar PPP mai adawa Oumar Jallow ya ce ya kasa gane dalilin da ya sa Jammeh yake maganar zuwa kotu, amma a matsayinsu na gungun jam'yyun adawa ba za su amince da komai ba face ya mika mulki ga zababben shugaban kasa da zarar wa'adin mulkinsa ya kare.
"Halayyar da Shugaba Jammeh ya nuna tamkar wani dan mulki kamakarya ne da ba ya son ya saki ragamar mulki cikin kwanciyar hankali da lumana ta hanyar demokaradiyya. Kundin tsarin mulkin Gambiya ya tanadi gudanar da zabukan kasar ta hannun hukumar zabe mai zaman kanta, wanda kuma mun yi nasara, wannan hukumar zaben wasu daga cikin mambobinta mutane ne wadanda Yahya Jammeh ya nada tun shekaru 15 da suka gabata, kuma zabukan da Yahya Jammeh ya yi nasara wannan hukuma ce dai ta shirya zabukan, kuma ta bayyana, a saboda haka me ya sa a yanzu zai nuna shakku a kanta?"
Hadakar Jam'iyun adawa da suka zabi Adama Barow sun bukaci da Shugaba Yahya Jammeh ya mika mulki ga sabon shugaba. Adama Barow ya shaida wa magoya bayansa cewa Shugaba Jammeh ba shi da ikon bada umarnin sake gudanar da sabon zabe.
"An kammala zabe yanzu ni ne sabon shugaban kasa mai jiran gado. Ina kira ga Shugaba Jammeh ya sauya matsayinsa ya amince da zabin da 'yan Gambiya suka yi domin wanzar da makoma mai kyau ga 'yan kasarmu wadanda suka cancanci samun samun cikakken 'yanci"
Kungiyar Tarayyar Afirka da sauran kasashen Afirka da na Turai sun yi tir da matakin da Yahya Jammmeh ya dauka, inda suka bukaci da ya mika mulki cikin ruwan sanyi.