Gambiya ta aiwatar da hukuncin kisa
August 25, 2012Shugaban jami'iyyar adawan Gambiya Ousainou Darboe, yayi kira ga ƙasashen duniya da su kakaba wa shugaba Yahya Jammeh takunkumi, idan rahotannin cewar ya fara aiwatar da hukuncin kisa akan prisononin ƙasar suka tabbata gaskiya. Shugaban jam'iyyar Demokraɗiyya Darboe, ya faɗa wa kamfanin dillancin labaru na AFP cewar, lokaci yayi da ƙasashen duniya zasu ɗauki matakan da zasu tilasta wa shugaba Jammeh daraja wa dokokin ƙasa da ƙasa. Ƙungiyar kare hakkin jama'a ta Amnesty International ta ruwaito cewar, a daren juma'a ce aka zartar da hukuncin kisa akan wasu prisononi guda tara, kasa da mako guda da alkawarin shugaba Jammeh, na rataye dukkan prisononin da aka yanke wa hukuncin kisa, waɗanda yawansu yakai 50. Rahotanni daga birnin Banjul wanda kuma ba'a tabbatar dasu ba, na nuna cewar an zartar da hukuncin kisa na farko ne, yini guda bayan ziyarar jakadan ƙungiyar Gamayyar Afirka Gambiya domin rokon shugaba Yayah Jammeh, da kada ya aiwatar da hukuncin kisa kamar yadda ya alkawarta. Ƙungiyar kare hakkin jama'a ta ƙasa da ƙasa ta Amnesty ta sanar da samun sahihan rahotanni dake nuni da yadda gwamnatin Gambiyan ta zartar da hukuncin kisa akan prisononi 9, batu dake nuni da cewar sauran waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa na fuskantar barazanar ratayewa, nan bada jimawa ba.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Saleh Umar Saleh