Gambiya na son a tuhumi Yahya Jammeh
November 4, 2022Ma'aikatar shari'ar Gambiya ce ta bukaci taimakon Kungiyar ECOWAS kan ta samar da kotun hadin gambiza da za ta gudanar da shari'ar take hakkin dan adam da aka aiktata a cikin shekaru 22 na mulkin tsohon shugaban kasar Yahya Jameh. Dama dai sunan tsohon shugaban na daga cikin sunayen mutane 69 da hukumar sassanci ta kasar ta fitar na wadanda suka take hakokkin jama'a.
An kwashe tsawon shekara guda da hukumar sassanci ta kasar Gambiya ta fitar da rahoton wadanda suka aikata laifukan take hakkin dan adam da suka hada da fyade da azabatar da jama'a baya ga wasu mutane da dama sun yi batan dabo a lokacin mulkin shugaban kama karya na kasar Yahya Jameh sai dai kawo yanzu babu wani tabbas a kan gurfanar da wadanda ake zargin.
Kasar ta Gambiya a yanzu ta na ganin mika bukatar neman taimakon kafa kotun hadin gambiza ga Kungiyar kasashen yammacin Afirka ECOWAS ita ce mafuta wajen cimma bukatarta a cewar babban lauyan gwamnati kana ministan shari'ah na kasar Dawda Jallow.
Ministan ya jadadda bukatar kafa wancan kotun, wanda a cewarsa kotunan Gambiya ba su da hurumi ko ma karfin ikon yanke hukunci kan wasu munanan laifuka da aikata a lokacin mulkin tsohon shugaban. Jallow ya kuma tabbatar da cewa, Gambiya na kokarin neman a mika mata Jammeh da ke gudun hijira a kasar Equatorial Gini.
Yayin da kasar Gambiyar ke dakon kafa wannan tsarin shari'ar a hukumance, suma wadanda abun ya shafa na fatan ganin hakan ya tabbata cikin kankanin lokaci. Masana kimiyyar siyasa a kasar irinsu Sait Matty Jaw na yaba wa gwamnatin kasar kan wannan yunkuri da take shirin yi don hada gwiwa da ECOWAS wajen gudanar da shari'ar Yahya Jameh.
Daga cikin wadanda suka fito fili suka amince da tuhumar da ake musu, sun ce, sun aikata laifukan azabar da jama'a da kuma kashe su a wancan lokacin bisa umurnin tsohon shugaban. A halin yanzu, wasu daga cikin gungun bata gari na gwamnatin Jammeh na fuskantar shari'a a nan Jamus da kuma Switzerland yayin da ake sa ran sauran su girbi abin da suka shuka a Gambiyar.