Gambiya ta raba gari da Taiwan
November 15, 2013Kasar Gambiya ta katse huldarta ta dipolomasiya da Taiwan bayan da suka shafe shekaru 18 suna dasawa da juna. Cikin wata sanarwa, shugaba Yahya Jammeh ya bayyana cewa ya dauki wannan matakin ne domin kare mutunci kasarsa, da ke zama daya daga cikin mafi karanci a nahiyar afirka.
Da ma dai Gambiya na daga cikin kasashen Afirka uku da suka hada da Burkina Faso da kuma Swaziland, da suka amince da Taiwan a matsayin kasa mai cin gashin kanta bayan da ta balle daga china.
Ita dai kasar Taiwan ta nuna bakin cikinta game da wannan mataki da Gambiya ta dauka. Yayin da china ta nuna mamaki tare da nesanta kanta daga wannan mataki. Sai dai kuma hukumomin Beijing ba su bayyana ku suna da niyar kullu huldar jakadanci da Gambiya ba koko a'a.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Umaru Aliyu