Gambiya ta shiga rudani bayan Jammeh ya lashe amansa
December 10, 2016Bayan kuwa tun da fari ya ce ya amince da shan kaye, Shugaba Jammeh dai a wani jawabi da ya gabatar ta kafar yada labarai ya ce a bangaren hukumar zaben kasar ta Gambiya an samu kuskure a kirga kur'iun da ya ba wa Adama Barrow na bangaren adawa mulki, dan haka ya soke zaben.
"Na sanar da al'ummar kasar Gambiya cewa na watsar da sakamakon zaben dan haka za a sake komawa akwatunan kada kuri'a dan na tabbatar da cewa kowane dan Gambiya ya kada kuri'a kuma an mutuntata."
Shugaba Jammeh mai shekaru 22 ya na kan mulki a Gambiya, ya amince da hukumar zaben kasar, hakan ya sa ya amince da shan kaye a cewarsa, amma gano wannan kuskure na kirgen kuri'u ya sanya ya sauya matsaya. Kuma ya ce kasashen waje na katsa landan a kasarsa har da sa baki a harkokin zabenta don haka bai zai lamunci hukumar zabe wacce ta dauki bangare ba.