Gambiya ta zama Jamhuriyar Musulunci
December 12, 2015Fadar shugaban kasar ta Gambiya ce ta tabbatar matakin mayar da Gambiya Jamhuriyar Musulunci a wannan Asabar. Dan shekaru 50 da haihuwa kuma wanda ya yi ayyukan soja, shugaban na Gambiya Yahya Jammeh ya ce makomar kasar na a hannun Allah, inda ya ce daga wannan rana kasar Gambiya ta koma Jamhuriyar Muslunci cikin wani jawabi da ya yi a birnin Brufut da ke a nisan km 25 da Banjul babban birnin kasar. Sai dai kawo yanzu babu wani labari kan matakan da kasar ta Gambiya ta dauka na wannan sauyi.
Kasar ta Gambiya dai wadda kasar Birtaniya ta yi mata mulkin mallaka, na da al'umma akalla miliyan daya da dubu dari tara da tasa'in da shida, kuma kashi 90 cikin 100 na 'yan kasar Musulmai ne. Ana ganin shugaba Yahya Jammeh rike da Alkur'ani mai tsarki da kuma calbi a hannunsa.