1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gambiya za ta zabi sabuwar majalisa

March 29, 2012

A'lumar Gambiya na kada kuri'a a zaben majalisa da tuni aka san yadda sakamakonsa zai kaya

https://p.dw.com/p/14UlJ
An election worker displays marbles cast for President Yaya Jammeh at one polling station to political party representatives during vote counting in Banjul, Gambia Friday, Sept. 22, 2006. Gambians voted for president Friday, dropping a marble into a bin marked with their candidate's color, in elections that longtime President Yaya Jammeh is widely expected to win. (ddp images/AP Photo/Rebecca Blackwell) bpk / Gerhard Kiesling
Hoto: AP

A kasar Gambiya yau, 29-03-2012 ne ake gudanar da zaben majalisar dokoki - zaben da yan adawa suka kaurace wa suna masu zargin gwamnatin da murda tsarinsa.

Su dai al'umar kasar ta Gambiya suna amfani da wannan tsari ne na musamman sakamakon rashin iya rubutu ko karatu. Bukatar canja wannan tsari na daya daga cikin bukatun 14 da 'yan adawa suka mika wa Shugaba Yahya Jammeh. Rashin samun wannan sauyi ne ma ya sa 'yan adawar suka kaurace wa zaben. Ga dai bayanin da Ousman Silleh editan jaridar Forayya mai zaman kanta a kasar ta Gambiya ya yi game da wannan tsari. Ya ce:

"Idan ka samu sunanka akan rajsta sai a baka wata 'yar takarda da za ka kada a cikin ganga. Ko wane dan takara dai na da tasa gangar. Saboda haka kowa sai kada takardarsa ne a cikin gangar dan takarar da yake so. Ta haka ne dai ake gudanar da zaben wanda bayan kawo karshensa za a kidaya takardun kowane dan takara sannan a bayana wanda ya lashe zaben."

Supporters of President Yaya Jammeh gather on the beach in front of his residence to celebrate his reelection, in Banjul, Gambia Saturday, Sept. 23, 2006. Thousands of people turned out to celebrate Jammeh's election to a third term. (AP Photo/Rebecca Blackwell)
Hoto: AP

Ousman Silleh ya ce rashin sauya wannan tsari ne dalilin da ya sa jam'iyyun adawar kasar suka kaurace wa zaben.

"Jam'iyyu shida daga cikin jam'iyyun kasar guda bakwai ne suka kaurace wa wannan zabe da suka yi kira ga hukumar zaben kasar da ta dakatar da shi. kusan rabin kujerun majalisar babu takara akansu. Wasu 'yan takaran ma mambobin ne na jam'iyyar da ke mulki. To amma sai suka ki tsayawa a karkashin tutar jam'iyyar. Dalili kenan da ya sa suka tsaya a matsayin 'yan takarar da ba su karkashin wata jam'iyya.

DW ta tuntubi 'yan takarar don jin dalilinsu na kin tsayawa. To amma sai suka ki su yi magana. Kungiyar ECOWAS dai ta nuna rashin amincewarta da wannan zabe. A cikin jawabin da ta yi ana washe gari a gudanar da zaben kungiyar ta nunar da cewa zaben ba zai gudana a cikin yanayi na walawala da adalici ba. Kuma ko da yake kungiyar AU ta tura jami'anta domin sa ido akan zaben, to amma a cewar Heinrich Bergstraesser na cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa da ke Jamus babu abin da wadannan jami'an za su tabuka.

"Kungiyar ECOWAS ta ki ta tura 'yan sa ido a lokacin zaben shugaban kasa. Kuma duk da cewa kungiyar AU ta tura jami'anta to amma na san shugaba Jammeh zai yi aiki akansu saboda da yana sane da cewa jam'iyyarsa za ta samu gagarumar nasara ba da wani ka ce na ce ba- abin da zai ba shi damar aiwatar da sauye-sauye a kundin tsarin mulkin kasar a cikin sauki. Masu ruwa da tsaki a harkar zaben na kasa kasa kawai so suke sun gwada wa duniya alamun da ke nuni da cewa wannan zabe zai gudana akan turba ta dimukuradiya."

Gambia's President Al Hadji Yahya Jammeh addresses the United Nations General Assembly at the U.N. headquarters in New York, Monday, Sept. 19, 2005. (AP Photo/John Marshall Mantel)
Yahya JammehHoto: AP

shi dai shugaba Jammeh zai sake lashe zaben majalisar dokoki kuma babu wani sauyi da hakan zai samar. A don haka ne Heinrich Bergstraesser ke ganin cewa lokaci ya yi da gamayyar kasa da kasa za t a shiga kasar ta Gambiya domin nuna wa 'yan adawa cewa ba a mai da su sanyar ware ba.

Kuna iya sauraron sautin wannan rahoto daga kasa.

Mawallafi: Jessie Wingard/ Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani