Ganawar Paparoma Francis da Obama
March 27, 2014Paparoma Francis da Shugaba Obama na Amirka sun gana a karon farko a wannan alhamis a fadan Vatican, inda tattaunawarsu ya mayar da hankali kan yaki da rashin daidaito da kuma sulhunta rikice-rikicen da suka addabi mafi yawan kasashen duniya.
Paparoman da Obama sun kuma yi wata ganawar da ta dauki mointoci 50 inda daga bisani ya gana da Sakataren kula da harkokin wajen fadar Vatican Cardinal Pietro Parolin.
A wata hira da yayi da jaridar Corriere della Sera Obama ya yabi Paparoma Francis musamman saboda irin karfi gwiwar da ya baiwa mutane a duk fadin duniya a abin da ya kwatanta da sadaukar da kan da yayi wajen ganin an kamanta adalci a al'umma da kuma sakonsa na kauna da tausayi.
Manyan jami'an biyu dai sun tattauna batun sulhu tsakanin Falasdinu da Israila, da rikicin Siriya da ma na baya-bayan nan wato halin da ake ciki a Ukraine.
Shugaban na Amirka ya yada zango ne a birnin Rome, a ziyarar da yake yi a nahiyar Turai inda ya je kasashen Holland da Beljiyam. Bayan Fadan na Vaticam, Obaman ya amsa goron gayyatar zuwa cin abincin rana da shugaban kasra Italiya Giorgio Napolitano inda daga nan zai gana da sabon firaminista Matteo Renzi.
Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal