1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gangamin neman agaji ga 'yan gudun hijra Falasdinu

Ramatu Garba Baba
March 14, 2018

Shugabanin kasashen duniya masu fada a ji za su gudanar da wani taro a gobe Alhamis don tattauna batun samar da kudi bayan da Amirka ta sanar da janye tallafin da ta ke bai wa 'yan gudun hijrar Falasdinu.

https://p.dw.com/p/2uHTz
Gazastreifen UNRWA Protest  Versorgung Palästinenser
Hoto: Reuters/I. Abu Mustafa

Janye tallafin kudin da Amirka wacce ta fi kowacce kasa bayar da kaso mafi tsoka, ya jefa rayuwar 'yan gudun hijrar da suka haura miliyan uku cikin garari da kuma bukatar taimakon gaggawa. Taron da zai gudana a birnin Roma zai meka kokon bara ga Turai da ma kasashen yankin Gulf don cike gibin da aka samu a sanadiyar matakin da shugaban Amirka Donald Trump ya dauka na katse bayar da tallafin.

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da 'yan gudun hijra Falasdinu ta baiyana cewa za ta shirya gangami na neman agajin kudi na musanman a yayin wannan taron don rage radadin da ake fuskanta, babban burinsu inji hukumar shi ne na ganin al'umomin kasa da kasa sun bayar da tallafin da ya dace don kare hakki dama mutuncin 'yan gudun hijrar Falasdinawan.