1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sokoto: Garejin gyaran mota na mata kanikawa

April 6, 2021

A Sokoto karon farko an bude garejin gyaran motoci na zallar mata kanikawa, a kokarin bai wa mata masu motoci dama da kuma sakewa a yayin da suka kai gyaran motocinsu ga takwarorinsu mata.

https://p.dw.com/p/3rdNt
Afrika Nigeria Sokoto Automechanikerinnen
Hoto: Ma'awiyya Abubakar Sidiq/DW

Shi dai wannan garejin zallar kanikawa mata mai suna Nana Female Mechanic Garage a turance tuni ya soma aiki gadan-gadan inda kuma suke duba tare da gyara motoci dabam-dabam. An bude  garejin ne a cikin birnin Sokoto da ke arewacin Najeriya da manufar saukaka wa mata masu motoci da zai ba su damar kai motocinsu don gyarawa.

Hindatu Dayyabu ita ce shugabar da ke kula da wannan garejin ta mata zalla ta kuma bayyana makasudin bude garejin.

Afrika Nigeria Sokoto Automechanikerinnen
Hoto: Ma'awiyya Abubakar Sidiq/DW

"Da farko dai mun bude wannan gareji ne don kirkiro aikin yi ga mata, na biyu akwai mata da yawa da ke da motoci amma suna samun matsala wajen kai motocinsu gyara, saboda da yawa garejin gyaran mota maza ne ke aiki a ciki. Buden wannan na kanikawa mata zalla, zai ba wa matan kwarin gwiwa ya kuma kawo musu sauki wajen kai gyaran motocinsu."

Yanzu haka dai al'ummar jihar Sokoto na cike da mamaki na wannan garejin mata zalla abin da ya sanya mutane da dama ke ta tururuwa don ganewa idonsu zahirin yadda karon farko matan ke gudanar da wannan sana'a ta gyaran motoci da ba kasafai aka saba ganin ta ba a yankunan kasar Hausa.      

Wasu daga cikin mata kanikawa sun ce da ma suna da ra'ayin aikin gyaran mota a ransu. Aikin na su na tafiya daidai yadda ya kamata. Suna kuma jin dadin aikin.

Afrika Nigeria Sokoto Automechanikerinnen
Hoto: Ma'awiyya Abubakar Sidiq/DW

Suna gyaran injin mota da abin ya shafi kafar mota da radiyeto da sauransu.

To amma kuma tuni mahukuntan wannan gareji ta mata suka soma wani aikin bayar da horo lokaci zuwa lokaci ga mata da 'yan mata don su kwaikwayi wannan sana'a ta gayaran motoci.

Wata da ta kai motarta gyara ta gamsu ta kuma yaba da aikin mata kanikawan.

Ko ba komai ana ganin wannan sabuwar garejin kanikawa mata zalla ya samar da wasu gurabun ayukkan yi da kuma sahalewa mata masu motoci sauki na garzayawa wurin ba tare da wata fargaba ba.