Gargaɗin 'yan tawayen Siriya
January 20, 2014Haɗin kan ƙungiyoyin 'yan tawaye a Siriya sun yi gargaɗin cewa babbar ƙungiyar 'yan adawar ƙasar ba ta da hurumin yanke shawara kan abin da 'yan ƙasa ke buƙata idan har suka tafi taron sulhun na Geneva.
Sun kuma ƙara da cewa hafsoshin tsaron ƙasar da ma sauran 'yan siyasa basu baiwa kowace jami'yya ikon yin amfani da bakin 'yan ƙasa wajen cin albasa ba, bare ma har su amince da wasu sharuɗɗan da aka iya gindaya musu wajen taron da ake sa ran gudanarwa cikin wannan makon.
Kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA ya rawaito cewa ƙungiyoyin 'yan tawayen sun ce za su amince su cimma matsaya a siyasance ne kaɗai idan har aka sako fursunonin da aka ƙulle, aka tsige gwamnati aka kuma tuhume ta da duk laifukan da ta aikata.
Duk wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Amirka da Majalisar Dinkin Duniya ke ƙoƙarin ganin an gudanar da tattaunawar sulhun da a wani mataki na bazata ya kama hanyar shiriricewa bayan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta miƙa goron gayyatar taron ga ƙasar Iran.
Da ma dai da ƙyar da suɗin goshi, 'yan adawan Siriyan waɗanda ke fama da rarrabuwan kawuna suka amince su je taron da akewa laƙabi da Geneva II, kuma yanzu suna barazanar ƙauracewa idan har ba a janye goron gayyatar da aka miƙawa mahukuntan na Tehran ba.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu