WHO na son kasashe su kara sanya ido kan Covid-19
April 20, 2020Talla
Wannan gargadi na zuwa ne a yayin da a wannan Litinin wasu kasashen duniya musamman a nahiyar Turai ke shirin fara sassauta dokokin da suka sanya na rage yaduwar cutar.
Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya shaida wa wani taron ministocin kiwon lafiya na kasashe masu tattalin arzikin duniya na G20 cewa duk da cewa akwai karfafa gwiwa aji cewa kasashe za su fara komawa kamar yadda ake rayuwa a baya, amma a sanya ido sosai domin wannan ba ya nufin cewa ba za a samu karin barkewar cutar a kasashen ba, yana mai gargadin kasashen da su kasance a cikin shirin ko-ta-kwana.
Kasashen da ke da burin fara sassauta dokar kulle daga Litinin din nan sun hada da Jamus da Czech Republic da Faransa da Norway da Albania da kuma Poland.