Gargaɗin Faransa bayan cafke 'yar ƙasar a Kenya
October 1, 2011Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta gargaɗi 'yan ƙasarta da su guje ma sansani shaƙatawa na lamu da ke kenya, bayan da wasu 'yan bindiga suka cafke wata tsohuwa mai fama da naƙasa a gidanta da ke gabashin ƙasar. Gwamnatin Kenya ta bayyana cewa wasu 'yan Somaliya goma ɗauke da makamai, waɗanda kuma ake kyautata zaton cewar 'yan ƙungiyar al-Shabab ne suka sace matar mai shekara 66 da haihuwa da misalin ƙarfe uku da rabi na dare.
Rahotannin sun nunar da cewa da dama daga cikin 'yan bindigan sun jikata a lokacin da suka yi misayar wuta da jami'an tsaron kenya, yayin da wasunsu kuma suka ranta a na kare.Wannan dai shine karo na biyu a cikin kwanaki talatain na baya-bayannan, da ake yin garkuwa da turawa na kasashen ketare a wannan yanki dake kusa da iyakar ƙasar Somaliya. A farkon watan Satumban da ya gabata ma dai, 'yan bingida dagan Somaliya sun hallaka wani ɗan ƙasar Ingila ɗaya, tare da yin garkuwa da matarsa.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal