Interventionen und Interessenskollisionen
March 19, 2013Duk da nasarar da kasashen duniya suka yi na kawo karshen yakin cacar baka, amma suna ci gaba da samun rarrabuwar kawuna dangane da hanyoyin warware rigingimu a sassa daban daban na duniya. Yakin da ke ci gaba da wanzuwa a kasar Siriya, babban misali ne ga rashin daidaiton ra'ayin kasashen.
Cibiyar gudanar da bincike kan rikice rikice ta kasa da kasa dake Heidelberg anan Jamus ta ruwaito cewar, a shekara ta 2012 kadai an samu barkewar rigingimu 396, karin 11 kenan akan na shekara ta 2011.
A yanzun na da ake batu kuma dalar Amirka miliyan dubu bakwai da miliyan 230 ne kasashen duniya suka kasafta domin gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya a yankunan da ake fama da rigingimu da kuma yake yake, inda kasashen Amirka da Japan da Birtaniya game da Jamus ke sahun farko wajen bayar da gudummowa. Sai dai bisa la'akari da dimbin kudin da ake kashewa ne yasa kasashe musamman na yammacin duniya ke lalubo hanyar sake fasalin tinkarar matsalar, inda rikicin Siriya ke zama daya daga cikin misalai na iyakar da kasashe ke da ita a kokarin shawo kan rigingimun.
A cewar masanin kimiyyar siyasa Cristian Mölling da ke gidauniyar kimiyya da siyasa anan Jamus, banbancin akidu ne ya hana warware rikici irin na Siriya:
Ya ce "Dole ne mutum ya san cewar a lokacin da ake shiga tsakani ko matakin soji ne aka dauka ko na farar hula mutum zai yi aiki ne da bangarorin kasa da kasa da dama saboda haka dole mutum ya hada kai da su. Hadin kai a waje guda shi ne mabudi, a daya wajen kuma shi ne babbar matsalar shiga tsakani saboda dukkan bagarorin na da manufofin da suka sabawa juna. Saboda haka dole mutum ya yi kokarin nazarin manufofin, wannan na nufin cewar dole a cimma daidato."
Masu ruwa da tsaki a rikicin Siriya
Banbancin manufofi game da rikicin na Siriya ne ya sa kasashen Saudiyya da Turkiyya da Qatar komawa gefe guda tare da Amirka da kuma kasashen Turai wajen tallafawa 'yan tawayen Siriya, yayin da kasashen Rasha da China da Iran game da Iraqi, ke daya bangaren da ke nuna goyon baya ga gwamnatin shugaba Bashar al-Assad na Siriya.
Sai dai kuma duk da bukatar tallafawa 'yan tawaye da makamai da kasashen Birtaniya da Faransa ke jagoranta hakar ba ta cimma ruwa ba tukuna a zahiri, wanda kuma masanin kimiyyar siyasa Cristian Mölling ya ce abin a yi masa nazari ne:
Ya ce " A baya dai mun yi nazarin ayar tambaya dangane da yadda za'a kawar da tsoma bakin soji ko kuma farar hula cikin lamuran da suka danganci zamantakewa da siyasa, ko kuma takaita shi. kasancewar wannan dama yana da iyaka. Domin da farko dai akwai al'ummar kasar da kansu dama abokan kawancen siyasa suna dab da kaiwa wannan iyaka dangane da tsoma baki a matakin kasa da kasa. A daya hannun kuma akwai su kansu abokan kawancen na ketare."
Kasashen da ke goyon bayan 'yan tawaye a rikicin Siriya dai na tababar ba su makamai domin gudun fadawa a hannun masu kishin addinin da ke bangaren 'yan tawayen, da kuma irin darasin da suka koya daga rikicin Libiya, inda masu tada tarzoma suka mallaki muggan makaman da suke kai farmaki akan muradun kasashen yamma. Sai kuma batun hana yaduwar rikicin a daukacin yankin na Gabbas Ta Tsakiya.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab Mohammed Abubakar