1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Gaza zai iya ruruta rikicin Isra'ila da Hezbollah

October 12, 2023

Hezbullah ko Isra'ila ba sa muradin ganin ruruwar wutar sabon tashin hankali ya kunno kai a kusa da iyakar Lebanon, Sai dai killace Gaza da Isra'ila ta yi bayan hare-haren Hamas na iya sauya lamarin cikin kankanin lokaci

https://p.dw.com/p/4XT9s
Isra'ila ta kara yawan sojojinta a kusa da kan iyaka da Lebanon bayan wasu hare-haren Hezbullah
Isra'ila ta kara yawan sojojinta a kusa da kan iyaka da Lebanon bayan wasu hare-haren Hezbullah Hoto: JALAA MAREY/AFP

A manyan titunan da suka taso daga kudancin Lebanon zuwa Beirut babban birnin kasar, akwai cunkoson motoci tun ma kafin a fara fada tsakanin dakarun sojin Isra'ila da kungiyar Hizbullah da ke samun goyon bayan Iran, a kusa da kan iyakar Lebanon da Isra'ila. Rahotanni na nuni da cewar, dubban mutane daga kudanci sun bar yankin saboda tsoro da fargabar abin da zai iya faruwa a wannan rikici. Mariam Hoteit, wata mai 'ya'ya biyar daga garin Shakra, wanda ke da tazarar kilomita 7 kawai daga kan iyaka da Isra'ila, ta shaida wa. DW cewar a kan han hanyarsu zuwa Beirut, sun yi mamakin yawan motocin da ke kan hanya. Ta ce hakan ya tunatar da ita abubuwan da suka faru a lokacin da suka fuskanci karancin mai a bara.

Kelly Petillo, mai bincike ce ta Lebanon, kan harkokin waje a majalisar Turai ne cewa: "Wannan yana nufin duk bangarorin biyu suna taka-tsantsan kuma suna sane da iyakarsu idan aka zo batun rikici da juna. Ya zuwa yanzu suna kokarin ganin cewar babu wanda ya tsallaka layi. Misali, jan layi ga Hezbollah na iya kasancewa idan tashe-tashen hankula suka tsananta a Gaza, lamura na iyYakin Gabas ta Tsakiya ya dauki hankalia yin tsanani a bangarenta."

Karin bayanYakin Gabas ta Tsakiya ya dauki hankalii:  

Lebanon na fama da rikicin tattalin arziki da siyasa, wanda ya share fagen samar da wata kasa a cikin wata kasa ta Hezbullah.
Lebanon na fama da rikicin tattalin arziki da siyasa, wanda ya share fagen samar da wata kasa a cikin wata kasa ta Hizbullah.Hoto: MOHAMED AZAKIR/REUTERS

Kungiyar Hezbullah ta rabu gida biyu, bangaren siyasa da na soji, inda Kungiyar Tarayyar Turai da Faransa da Kosovo da sauran gwamnatoci suka ayyana bangaren sojin a matsayin kungiyar ta'addanci. A yayin da kasashen Amurka da Jamus da Isra'ila da wasu gwamnatoci da dama suka ayyana kungiyar ta Hezbullah baki dayana a matsayin kungiyar ta'addanci.

Hezbullah na da tasiri sosai a harkokin siyasa da rayuwar jama'ar Lebanon. Kungiyar na da kashi 12% na kujerun majalisar dokoki a kasar Lebanon, kuma ko bayan faduwar gwamnati bayan zaben shekara ta 2022, tana da alaka ta kut da kut da jam'iyyun da ke mulki. Ita ce ke ba da kudin asibitoci kuma tana gudanar da nata bankuna da kanta, inda take da damar samun dalar Amurka.

Karin bayani: Jamus ta dakatar da tallafi ga Falasdinawa 

Libanon-Israel-Konflikt Hisbollah | Kundgebung Hisbollah-Anhänger
An takaita kai hare-hare daga bangarorin biyu , ko da yake sojojin Isra'ila sun kashe mayakan Hezbullah biyu, yayin da wani sojan Isra'ila guda ya jikkata .Hoto: Hussein Malla/AP/picture alliance

Sai dai ga manazarta irin Nathan Brown, farfesa a kimiyyar siyasa da al'amuran duniya a Jami'ar George Washington, akwai bukatar daukar matakan kauce wa komawa sabon rikici da zai barke tsakanin Hezbullah da Isra'ila: Ya ce: "Ba na tsammanin Isra'ila za ta fara neman tashin hankali amma idan Hezbollah ta yi, Isra'ila za ta iya mayar da martani da karfi, bisa imanin nuna cewar dole ne a tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, don haka akwai yiwuwar ta'azzarawr rikicin".

Idan aka yi la'akari da irin muhimmancin da kungiyar ke da shi a siyasance da bangaren soja a kasar Lebanon, yana da kyau a ce shugabancinta na zuba ido sosai a yayin da al'amura ke faruwa a Isra'ila da Gaza, kuma kungiyar da ke samun goyon bayan Iran, wadda EU da Amurka da Jamus da wasu gwamnatoci suka ayyana a matsayin kungiyar ta'addanci sun kai wani babban hari a kan Isra'ila a ranar Asabar.