1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Senegal ta taimaka a rikicin ECOWAS

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 17, 2024

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya bukaci takwaransa na Senegal Bassirou Diomaye Faye da ke ziyara a yanzu haka a Accra, ya taimaka a shawo kan rikicin kungiyar ECOWAS da kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar.

https://p.dw.com/p/4g19L
Ghana | Nana Akufo-Addo | Ziyara | Senegal | Bassirou Diomaye Faye | ECOWAS
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo Hoto: Michael Kappeler/dpa

Shugaba Nana Akufo-Addo ya yi wannan kiran ne jim kakdan bayan tattaunwarsu da Shugaba Bassirou Diomaye Faye a Accra babban birnin kasarsa Ghana, inda ya ce sun yi sa'ar samun sabon shugaba da a tunaninsa zai taimaka wajen shawo kan matsalar wadannan kasashe uku na Mali da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar da suka ayyana ficewarasu daga kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO. A nasa jawabin mai shekaru 44 a duniya Shugaba Faye da ya isa Accra bayan kammala ziyarasa ga shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a Abuja, ya bayyana fatan cewa tare da tallafin Najeriyar da ke jagorancin shugabancin kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO a yanzu zai iya shawo kan kasashen uku su dawo gidansu na asali.