1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan aware sun kai hari kan motocin sufuri mallakin gwamnati

September 29, 2020

A Ghana kungiyar 'yan aware mai da’awar ballewa don kafa kasa mai cin gashin kanta a kan iyakar Ghana da Togo, ta kai hari kan motocin kamfanin sufurin motoci na gwamnati.

https://p.dw.com/p/3jBPf
Ghana Volta Region
Hoto: Elvis Washington

Majiyoyi sun bayyana cewar sai da membobin kungiyar suka ta harbin bindigogi kana suka fara lakada wa direbobin kamfanin sufurin motocin na gwamnati da aka fi sani da State Transport Company wato STC a takaice, dukar kawo wuka, a tashar motocin da ke birnin Ho, kana daga bisani suka kona motoci biyu kurmus. Wannan na zuwa ne kwanaki kalilan bayan hari na farko da suka kai yankin na Volta a ranar Juma'a da ta gabata, inda ta yi garkuwa da 'yan sanda uku ciki har da kwamishinan yankin, inda aka rasa rai daya kana uku suka jikkata. Wani ganau ya shaida yadda abin ya faru.

"Mun so fara aiki ne a lokacin da suka iso shi ya sa babu wani fasinja da lamarin ya rutsa da shi. Ba su bari mun shiga harabar kamfanin motocin na STC ba."

Prof. Sheikh Usman Bari, na zaman tsohon jami'in diplomassiya a nan Ghana, wanda ya yi tsokaci a game da al'amarin yana mai cewa babban karan tsaye a harkar tsaro da zaman lafiya a kasar Ghana. Dole gwamnati ta tashi tsaye ta nemo maganin warware wannan rikici da aka fara tun a 1994. Kamata ya yi gwamnati ta zauna da su a ji bukatunsu, don a san yadda za a bullo wa lamarin tun bai baci ya zama wani abu dabam ba."

Ministan yada labaran kasar Ghana, Kojo Oppong Nkrumah
Ministan yada labaran kasar Ghana, Kojo Oppong NkrumahHoto: Kojo Oppong-Nkrumah

A gefe guda kuma dai ministan yada labaran Ghana Kojo Oppong Nkrumah, ya musanta cewa al'amarin na faruwa ne sakamakon sakacin hukumomin tsaron kasar, hasali ma, sune suka tarwatsa aniyar kungiyar na dana wa muhimmun gadoji, da madatsun ruwa da kasuwanni bama-bamai. Haka ma da yunkurin sace ministoci.

Da ma dai masana harkokin tsaro sun bayyana cewar harin ranar Jumma'ar somin tabi ne.

Kawo yanzu ministan tsaron kasa bai ce uffan ba a game da wannan batu, bayan da ministan yada labaran Ghanan ya bayyana cewar har yanzu akwai barazanar da hukumomin kasar ke kokarin dakilewa.

Ya zuwa wannan lokaci mutane 31 ne ake tsare da su ciki har da wata matashiya 'yar shekaru 19 kuma a ranar 13 ga watan Oktoba mai kamawa za su gurfana a gaban kuliya.