Gidauniyar Jamus ta taimaka wa kauyukan Najeriya
December 31, 2019A wani mataki na ganin an rage matsalolin karancin ruwan sha a yankunan karkara, Gidauniyar Robert Bosch ta kasar Jamus tare da hadin gwiwar gidauniyar samar da zaman lafiya ta duniya ''Global Peace Foundation'' sun gyara wa wasu mazauna kauyukan garuruwan kudancin Kaduna rijiyoyin burtsatsansu da suka lalace, tare kuma da koya masu yadda za su rika lura da gyara rijiyoyin da kansu ta hanyar aikin gayya.
Mata da kananan yara masu yawa ne suka yi tururuwa domin nuna murnnarsu inda suka yi bikin bude wani tsohon fanfon ruwan sha da wasu rijiyoyin burtsatsai guda shida da suka lalace tsawon shekaru. Lamarin ya jefa daruruwan mazauna kauyukan da ke a karkashin masarautar Koningkon da ke a karamar hukumar Jama’a a yankin kudancin Kaduna fadawa cikin matsanancin karancin tsaftataccen ruwa. Karancin ruwan na sha ya tilasta su neman ruwa a busassun koramai da koguna da shiga dokar daji wajen zuwa bakin kogi, dan neman ruwan sha da na girke-girke da sauran bukatu na yau da kullum.
Reverend Joseph John Hayap shi ne wakilin Gidauniyar Robert Bosch ta kasar Jamus da kungiyoyin da ke fafatukar tabbatar da dorewar zaman lafiya a Najeriya da suka gudanar da wannan ayyuka da zimmar magance matsalolin da kananan yara da matan aure ke fama da su a kauyuka.
Sheikh Halliru Dan Maraya da ke wakiltan kungiyar 'Global Peace Foundation' a yankin arewa cewa ya yi muddin al‘umma na zama cikin lafiya, su da kansu ne za su ci gaba da bullo da hanyoyin inganta rayuwarsu da ma lafiyarsu. Garuruwan da ake gyara masu wadannan rigiyoyin burtsatsai dai sun hada da Banboma da Goska da ungunwar Fari da unguwar Bakin Kogi da kuma fanfon garin Koninkon. Wadanda suka gyara rijiyoyin birtsatsai dai sun wayar da kan alumma hanyoyin lura da su ta yadda za su jima suna samun amfani.
Gidauniyar Robert Bosch ta kasar Jamus, itace ke taimakawa da yawancin kayayyakin gyara wadannan rijiyoyin don rage cututtukan da mata da kananan yara ke fama da su saboda rashin tsaftatchen ruwan sha.