1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girka: An kama wadanda suka tada gobara

Ahmed Salisu
September 15, 2020

Jami'an tsaro a tsibirin Lesbos na kasar a Girka sun kama mutane biyar da ake zargi da haddasa gobarar da lalata sansanin 'yan gudun hijira na Moria da ke tsibirin.

https://p.dw.com/p/3iVD2
Griechenland, Lesbos: Brand im Flüchtlingslager Moria
Hoto: Reuters/E. Marcou

Har wa yau jami'an na tsaro sun ce suna neman karin mutum guda ruwa a jallo da ake zargin yana da hannu a tashin gobarar, sai dai ya zuwa yanzu ba su yi karin haske kan ko su waye mutanen ba.

Tashin gobarar dai ta haifar da kalubale babba musamman ma ta fuskar tsugunar da 'yan gudun hijrar wanda yawansu ya haura dubu goma sha biyu, amma mahukuntan na Girka sun samar musu da waje na wucin gadi da suka ce nan da mako guda za su kammala akin tsugunar da su.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Tarayyar Jamus ta ambata shirinta na karbar 'yan gudun hijirar kimanin dubu da dari biyar don tsugunar da su a kasarta.