1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girka: Gobara ta sa jama'a yin kaura

Abdullahi Tanko Bala
August 4, 2021

Jami'an tsaron gabar ruwa a tsibirin Evia na kasar Girka na taimakawa wajen kwashe mutanen da ke neman tsira daga wutar daji da ke cigaba da ruruwa a yankin.

https://p.dw.com/p/3yYTR
Waldbrände in Griechenland
Hoto: Lydia Veropoulou/ANE/Eurokinissi/picture alliance

Dubban jama'a na ta kokarin ficewa daga gidajensu domin tsira da rayuwarsu sakamakon tsananin zafi da ke kara rura gobarar daji a wasu yankuna na kasar Girka

Kasar ta Girka na fuskantar zafi mafi tsanani cikin fiye da shekaru 30 da suka gabata.

Gobarar wadda jami'an kwana kwana ke ta kokarin kashewa ba dare ba rana ta kone gidaje fiye da 90 da wuraren kasuwanci 27 da kuma motoci fiye da 80 a cewar ministan kare rayuwar al'umma Nikos Hardalias.

Bakin hayaki ya turnuke birnin Athens yayin da a waje guda jama'a ke fama da matsalolin numfashi.

An dai bukaci tsofaffi su zauna a cikin gidajensu.