1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girka za ta mayar da yan gudun hijira 10,000

Abdullahi Tanko Bala
October 1, 2019

Kasar Girka na son mayar da 'yan gudun hijira 10,000 zuwa Turkiyya bayan wata gobara da ta tashi a wani sansanin yan gudun hijira da ke makare da mutane domin rage cunkoso a sansanonin.

https://p.dw.com/p/3QXG4
Die Lage der Flüchtlinge auf Lesbos
Hoto: DW/D. Tosidis

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan hadarin gobara da ta kama a sansanin yan gudun hijira na Moria.


A cikin wata sanarwa bayan taron majalisar ministoci gwamnatin ta Girka ta ce tana fatan zuwa karshen shekarar 2020 za ta kammala mayar da yan gudun hijirar 10,000 zuwa kasar Turkiyya domin rage yawan yan gudun hijirar da ke makare a sansanoni.


Matakin na nuna alamun sauyin manufa yayin da Firaminista Kriasko Mitsotakis mai ra'ayin rikau ya fara aiwatar da wasu tsauraran dokoki na yadda yake tunkarar batun yan gudun hijira a kasar.