'Yan jarida na neman kyautata makomar aikinsu
June 20, 2022Wannan dai shi ne karon farko da aka hallara a birnin na Bonn tun bayan bullar COVID 19 shekaru biyu da suka gabata, inda aka rika taron ta yanar gizo. A jawabinsa na maraba babban darektan kafar yada labaru na DW Peter Limbourg ya kasa boye farin cikinsa na sake samun wannan dama na musayar bayanai da shawarwari tsakanin kwararru da ma'abokan huldar tashar DW.
Taron na wannan karon ya yi nazari ne kan hali na tsaka mai wuya da 'yan jarida da ma kafafen yada labaru suka tsinci kansu a yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula kamar Ukraine da yankin Gabas ta Tsakiya da yankin Sahel na Afirka da kuma arewacin tarayyar Najeriya. Halin da ke bukatar daukar matakai tun daga yanzu domin gyaran gobe kamar yadda taken taron na wannan shekara ya kasance "Shata kyakkyawar makoma".
Ministar al'adu da yada labaru ta Jamus Claudia Roth ta bayyana wa mahalarta taron na yini biyu irin kokarin da gwamnatoci da shugannin gwamnati ke yi na samar da karin kariya ga 'yan jarida da ke cikin hadari a yayin ayyukansu, kamar yadda taron ministocin kasashe masu karfin tattalin arziki na G7 ya cimma.
Yankin sahel na yammacin Afirka na cikin wurare mafi hadari ga 'yan jarida. Daura da hatsarin aikin akwai kuma matsala ta rashin samun bayanai saboda fargaba a bangaren mazauna yankin a cewar dan jarida daga birnin Yamai Sadou Aliza Mouktar..
Tun da farko fitacciyar 'yar jaridar kasar Philippines da ta samu lambar yabo kan zaman lafiya a bara Maria Ressa, ta bayyana kasarta da zama daya daga cikin inda ake gasa wa 'yan jarida tsakuwa a hannu, amma ta ci gaba da fafutukarta na wayar da kai kan muhimmancin fadin gaskiya komai dacinta da ma kuma 'yancin tofa albarkacin baki da dimokuradiyya a dukkan sassa na duniya.